‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Mutane 26 A Sokoto

Wasu ‘yan bindiga sun yi ta harbin kan-mai-uwa-da-wabi, inda hakan ya yi sandiyyar mutuwar akalla mutane 26.

Harin ya tarwatsa alummar garuruwan guda uku, to amma daga bisani an samu tattarar jama’a da jami’an tsaro, inda aka je neman gawarwaki, aka kuma samu 26 da aka yi musu jana’iza da yammacin Litinin.

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya dage gudanar da taron gangamin yakin neman zabensa da aka tsara gudanarwa a Goronyo dake makwabtaka da karamar hukumar Rabah da lamarin ya auku, inda kuma ya halarci jana’izar mamatan.

Ya jajantawa iyalai da al’ummar yankin akan wannan ibtila’in kuma ya yi alkawarin gwamantinsa zata ci gaba da daukar matakai na tabbatar da cewa an tsare al’umma da dukiyoyinsu. Yace shugabanni da jami’an tsaro na jihar Sakkwato da gwamnati suna iya kokarinsu wurin kawo karshen wannan lamari.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto Murtala Mani, na daga cikin wadanda suka halarci jana’izar, ya kuma ce jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu wajen yaki da ‘yan ta’adda a yankin. Ya kuma ce suna hadin gwiwa da sojoji da jami’an tsaron farin kaya domin wannan yaki.

Wannan ne karo na biyu da ake kai irin wannan harin a gundumar Gandi. An kai harin na farkon ne a garin Tabanni a ranar tara ga watan Yulin da ya gabata, wanda yayi sanadiyyar rasa rayuka 32.

More News

Mayaƙan ISWAP Sun Kashe DPO A Borno

Wasu ƴan bindiga da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne sun kashe wani babban jami'in ɗan sanda a arewacin jihar Borno. A cewar wasu rahotanni...

Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Bawa Gwamnati Wa’adin Ranar 31 Ga Watan Mayu Da Ta Janye Ƙarin KuÉ—in Wuta

Ƙungiyoyin Ƙwadago na  NLC da TUC sun bawa gwamnatin tarayya wa'adin ranar 31 ga watan Mayu kan ta janye ƙarin kuɗin wutar lantarki da...

Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Bawa Gwamnati Wa’adin Ranar 31 Ga Watan Mayu Da Ta Janye Ƙarin KuÉ—in Wuta

Ƙungiyoyin Ƙwadago na  NLC da TUC sun bawa gwamnatin tarayya wa'adin ranar 31 ga watan Mayu kan ta janye ƙarin kuɗin wutar lantarki da...

Matatar mai ta fatakwal za ta iya fara aiki a ƙarshen watan Yuni

Matatar mai ta Fatakwal mai tace mai ganga 210,000 a kowacce rana na iya fara aiki a karshen watan Yuli bayan dogon lokaci. Jami’in hulda...