
Wasu da ake zargin yan fashi da makami ne sun kashe wani malamin addinin musulunci, Ibrahim Albani a gidansa dake Gobona a unguwar Tabra a jihar Gombe.
Da yake tabbatar da labarin a ranar Alhamis , mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Gombe, Mahid Abubakar ya ce yan bindigar sun farma gidan marigayin da misalin karfe 3 na daren ranar Laraba.
Abubakar ya ce malamin ya rasa ransa lokacin da yayi kokarin bude fuskar daya daga cikin maharan hakan yasa ya soke shi da wuka da kuma sarar shi da adda
Wannan ne bayanin da matarsa ta yi wa yan sanda a cewar Abubakar.
Ya kara da cewa kwamishinan yan sandan jihar ya bada umarnin yin cikakken bincike domin kamawa tare da hukunta waɗanda suka aikata haka.
Har ila yau kwamishinan ya sanar da dokar hana fita daga 12 na dare zuwa 06 na safe saboda yadda yawan aikata laifuka ya karu a jihar.