‘Yan sanda sun kashe ‘barayin shanu’ 100 a Zamfara

'Yan sandan Najeriya

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Rundunar ‘yan sandan ta ce ta kashe barayin shanu da dama

‘Yan sandan Najeriya sun ce sun kashe ‘yan ta’adda 104 a jihar Zamfara bayan wata fafatawa da suka yi a karamar hukumar Birnin Magaji, sannan kuma suka lalata maboyar ‘yan fashin da dama.

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta ce jami’an tsaron sun kuma rusa sansanoni uku na barayin, sannan suka kwato shanu sama da 500 da wasu dabbobi da dama.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an kashe dan sandanta daya yayin kwantar baunar da aka yi musu, sai dai wasu majiyoyin gwamnatin jihar sun shaida wa BBC cewa an kashe ‘yan sanda da dama.

Lamarin dai ya faru ne da yammacin Alhamis din nan, yayin da jami’an ‘yan sanda na musamman ke sintiri a cikin dazuzzukan jihar ta Zamfara domin zakulo barayin shanu da masu garkuwa da mutane dake addabar sassan jihar da dama.
Haka kuma dakarun na musamman sun kama sama da mutum 85 da ake zargin gungun masu aikata miyagun laifuka ne a jihar.

Sanarwar ta ce an kuma kwato bindigogi kusan 80 da kuma wasu muggan makamai.

Sakamakon kwanton baunar dai rundunar ‘yan sandan kasar ta tura babban mataimakin sufeto janar domin zama babban kwamandan dakarun na musamman.

Babban aikin kwamandan shi ne maido da zaman lafiya a duka fadin Zamfara.

More from this stream

Recomended