’Yan Sanda Sun Kashe Babban Dan Bindiga a Abuja

Rundunar ’yan sandan birnin Tarayya, Abuja, ta bayyana cewa jami’anta sun kashe wani fitaccen ɗan bindiga mai garkuwa da mutane, Dogo Saleh.

Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta shaida wa manema labarai cewa Dogo Saleh da yaransa sun addabi wasu yankunan Abuja da hare-hare da sace mutane.

Ta ce bayan samun bayanan sirri kan maboyarsa, jami’an tsaro sun kai farmaki domin cafke shi.

“Sai dai yayin gumurzun harbe-harbe da jami’anmu, mun samu nasarar kashe ɗan bindigar tare da wasu daga cikin yaransa,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa Saleh, wanda ke matsayin mataimakin shugaban wata babbar ƙungiyar ’yan bindiga, ya shahara wajen aikata ta’addanci a kan titin Abuja zuwa Kaduna.

A lokacin arangamar, jami’an ’yan sanda sun ceto wasu mutanen da ’yan bindigan ke garkuwa da su.

More from this stream

Recomended