‘Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Kisan Wani Mai Sana’ar POS a Adamawa

Rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa ta bayyana cewa ta fara bincike kan kisan wani mai gudanar da hada-hadar POS mai suna Abbas Yuguda, mai shekaru 35, wanda wasu suka hallaka a karamar hukumar Mayo-Belwa.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 22 ga Maris, 2025, lokacin da wasu suka kai wa Yuguda farmaki da makamai masu hadari a hanyarsa ta dawowa gida bayan ya rufe kasuwancinsa.

A cewarsa, jami’an ‘yan sanda daga ofishin ‘yan sanda na Mayo-Belwa sun isa wurin da abin ya faru, sannan suka garzaya da Yuguda zuwa asibitin Cottage Hospital da ke Mayo-Belwa domin ceton rayuwarsa, amma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa yayin da ake masa jinya.

More from this stream

Recomended