‘Yan sanda sun kama mutum shida da ake zargi da kisan jami’ansu a Yobe

‘Yan sanda a Jihar Yobe sun cafke mutum shida da ake zargi da hannu a kisan wasu jami’ansu guda biyu a kauyen Kolere da ke karamar hukumar Fune.

Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da Ayyuka na Jihar Yobe, Abdu Abubakar Ozo, ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan wani taron tsaro da Mataimakin Gwamnan Jihar, Idi Barde Guban, ya jagoranta.

Ya ce wadanda aka kama suna da alaka da kisan jami’an, kuma yanzu haka suna hannun sashen binciken manyan laifuka na jihar (State CID) don ci gaba da bincike.

A cewar DCP Ozo, rundunar ‘yan sanda ta kara tura jami’anta domin ci gaba da farautar sauran da ake zargi da hannu a kisan jami’an biyu.

Idan za a iya tunawa, tun farko an ruwaito cewa wasu bata-gari sun kashe DSP Ali Pindar da DSP Jantuku Philibus a cikin shekarar nan yayin da suka yi kokarin cafke wasu ‘yan daba da ake zargi a yankin Kolere da ke karamar hukumar Fune.

More from this stream

Recomended