Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan wani dan kasar Sin mai suna Mr. Chen Wang, wanda ke aiki da kamfanin WH Great Resource Ltd da ke Ogere, Jihar Ogun.
Rahotanni sun bayyana cewa Mr. Wang, mai shekara 33 a duniya, an kashe shi ne a ofishinsa a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu, 2025, bayan da aka sace masa rai ta hanyar daba masa wuka har lahira.
A cewar rahotanni, ana zargin cewa wasu masoya biyu ne suka kashe mamacin, inda suka lalata na’urar tsaro ta kamfanin kafin su kutsa kai ofishinsa tare da kai masa hari. Bayan kisan, suka kwace makullan gidansa, suka yi masa fashin gida, sannan suka tsere daga jihar da kudin da suka sace.
Tun da fari, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun, SP Omolola Odutola, ta bayyana cewa ana gudanar da bincike tare da baza komar neman wadanda suka aikata laifin.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025, wacce Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda kuma Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa an kama wadanda ake zargin su ne Yunusa Abdullahi, mai shekara 25, da Peace Danlami, mai shekara 20, a Jos, Jihar Filato.
Adejobi ya ce an kama su ne a inda suke boye da wasu sabbin sunaye don kauce wa gano su.
A cewarsa, “Kama su ya biyo bayan hadin gwiwar aiki da bayanan sirri, tare da amfani da na’urorin zamani na bincike da tantance bayanai da kuma amfani da dabarun leƙen asiri.”
Sanarwar ta kara da cewa: “Dangane da matakin dabarun sintiri da Babban Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Egbetokun, ya dauka, an tura Rundunar Binciken Sirri ta Kasa (TIU) domin taimaka wa Sashen Binciken Laifuka na Jihar Ogun da kayan aiki da fasahar bincike.”
“Bayan makonni da dama na sa ido ta hanyar na’ura da dabarun aiki, jami’an da ke hedikwatar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sashen binciken manyan laifuka na jihar, sun kama Yunusa Abdullahi (namiji, daga Jihar Borno) da Peace Keno Danlami (mace, daga Jihar Taraba) a ranar 14 ga watan Yuli, 2025, a Jos, inda suke boye da sunaye na karya.”
Adejobi ya bayyana cewa ana ci gaba da tsare su, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
A karshe, IGP Kayode Egbetokun ya jinjinawa rundunar Jihar Ogun, da sashen binciken sirri, da dukkan jami’an da suka taka rawa a kama wadanda ake zargi, bisa kwazon su da jajircewarsu wajen tabbatar da gaskiya.
Ya kuma sake jaddada kudirin rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da baki mazauna Najeriya, ta hanyar amfani da dabarun sintiri da bincike na zamani.