‘Yan Sanda Sun Kama Masu Laifi 39 Bayan Sun Ceto Mutane 11 da Aka Sace a Jihar Legas

Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta sanar da cafke mutane 39 da ake zargi da aikata muggan laifuka daban-daban, da kuma ceto mutane 11 da aka sace, a wasu ayyukan sintiri da suka gudana cikin makonni biyu da suka gabata.

Kakakin rundunar, Chief Superintendent Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron manema labarai da ake yi kowanne mako biyu, inda ya wakilci Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Olohundare Moshood Jimoh.

Hundeyin ya ce, daga cikin laifukan da ake zargin mutanen sun hada da kisan kai, satar mutane, fashi da makami, fyade, satar yara, lalata kayan gwamnati, sarrafa gidan karuwai ba bisa ka’ida ba, mallakar makamai ba bisa doka ba, da kuma safarar miyagun kwayoyi.

A cewar rundunar, abubuwan da suka samu a hannun wadanda ake zargi sun hada da bindigogi 10, harsasai 49, babura biyu, mota daya, sandunan wutar titi da aka lalata, wayoyin sadarwa, wayoyi biyu, da wasu sinadarai masu hadari.

An kuma ceto mutane tara daga gidan, ciki har da mata guda shida da yara guda uku: Precious (24), Magdalene (25), Adaobi (23), Princess (22), Ifeanyi (25), Amaka (26), Destiny (7), Miracle (5), da Success (2).

More from this stream

Recomended