‘Yan sanda sun kama dagacin Guiwa da wasu mutane 13 bisa zargin taimaka wa ‘yan bindiga a jihar Neja

Rundunar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar masu gadi da mafarauta sun kama dagacin kauyen Guiwa da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja tare da wasu mutane 13 bisa zargin taimaka wa ‘yan bindiga.

Wani masani kan yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, 25 ga Mayu, 2025.

Makama ya ce bayanan sirri da ya samu sun nuna cewa jami’an tsaro sun kama dagacin, Garba Mohammed, ne a ranar 23 ga Mayu yayin wani atisayen kakkabe masu aikata laifuka da aka gudanar da hadin gwiwar ‘yan sanda, masu gadi, da kuma mafarauta.

An zargi dagacin da bayar da mafaka da kayan aiki ga ‘yan bindigar da ke addabar yankin.

Sauran wadanda aka kama sun hada da:

-Alhaji Abdullahi Shehu daga kauyen Wawa, karamar hukumar Borgu

-Umar Abubakar da Mohamadu Bako daga Gwajibo

-Shehu Alhaji Ardo daga Adogon Mallam

-Umar Abdullahi, Ibrahim Abubakar, Saidu Mohammed, Babuga Abdullahi, da Babuga Saidu daga Lumma

-Musa Mohammed daga Telle

-Mohammed Abubakar daga Dukku, karamar hukumar Rijau

-Molema Aliyu daga Pallagi

-Oro Abubakar daga Arera


Makama ya ce yayin bincike a gidan dagacin, jami’an tsaro sun gano babura hudu, harsashi daya da shanu goma da ake zargin ‘yan bindiga suka sace. Daga cikin shanun, uku da suka samu rauni an yanka su don gujewa wahala.

Wani jami’in ‘yan sanda daga jihar Neja ya shaida wa Makama cewa bincike na ci gaba da gudana kan lamarin.

More from this stream

Recomended