Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta samu nasarar ceto wani ɗalibi da aka sace daga Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi.
An gano cewa ɗalibin mai suna Augustine Madubiya, ɗan shekaru 23 da haihuwa kuma ɗalibi a sashen tattalin arziki na jami’ar, an ceto shi ba tare da rauni ba daga dajin Dakingari da sanyin safiyar Alhamis.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa: “Ceton ɗalibin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da rundunar ta samu.
“Bayan samun bayanan sirrin, DPO na Dakingari ya jagoranci hadakar jami’an ‘yan sanda da ‘yan sa-kai zuwa dajin domin gudanar da aikin ceto.”
Sanarwar ta ce a lokacin da masu garkuwa da mutane suka hango jami’an tsaro, sai suka bar ɗalibin suka tsere.
An sace Madubiya ne a ranar 8 ga Afrilu, 2025 a unguwar Jeji da ke cikin ƙaramar hukumar Kalgo a Jihar Kebbi.
Bayan ceto shi, an garzaya da shi zuwa cibiyar kiwon lafiya domin duba lafiyarsa, kuma rahotanni sun nuna yana cikin koshin lafiya. Za a mika shi ga iyalansa da zarar ya warke.
‘Yan Sanda Sun Ceto Ɗalibin Da Aka Sace a Jihar Kebbi
