Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta samu gagarumar nasara bayan da ta cafke wani shahararren dan fashi da makami wanda kuma ake zargin shugaban masu garkuwa da mutane ne, Abubakar Umar, wanda aka fi sani da Abu Dankano.
Rahotanni daga Zagazola Makama sun bayyana cewa an kama Abu Dankano ne a ranar 29 ga Maris, 2025, bayan da iyalan wani matashi mai shekaru 25, Badamasi Isiyaka, suka kai rahoton sace shi tun ranar 1 ga Maris.
Bayan kwana biyu da sace Isiyaka, masu garkuwar sun tuntubi iyalansa inda suka bukaci a biya su Naira miliyan talatin a matsayin kudin fansa.
Biyo bayan haka, jami’an ‘yan sanda sun kaddamar da wani kwararren shiri na bincike, wanda ya kai ga kama Umar mai shekaru 26, wanda ke zama a dajin Shimfida da ke karamar hukumar Jibia, wurin da ake yawan samun aikata laifuka.
A yayin bincike, Umar ya amsa laifinsa na hada kai wajen sace Badamasi Isiyaka, inda ya bayyana cewa yana da alaka da wasu fitattun shugabannin ‘yan bindiga irinsu Bello Turji, Dankarami, Na-Mardiyya, da Black.
‘Yan sanda sun bayyana cewa an samu nasarar ceto wanda aka sace ba tare da wani rauni ba, kuma suna ci gaba da kokarin kamo sauran wadanda suke da hannu a cikin lamarin.
‘Yan Sanda Sun Cafke Ƙasurgumin Dan Fashi Abu Dankano a Katsina
