Rundunar ‘Yan sandan Jihar Sakkwato ta bayyana cafke wasu mutane da ake zargi da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba tare da alaka da ta’addanci.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Ahmed Rufai, ya bayyana cewa jami’an Sashen Bincike na Sirri sun kama Bello Ibrahim, wanda aka fi sani da “Bello Currency”, tare da Alhaji Muhammad Danlato, Alhaji Abun Buhari, Alhaji Faruku Alhaji, da Abubakar Furniture.
Bincike ya gano cewa Bello Ibrahim na sayar da bindigogin da aka kera a nan gida ga sauran mutanen da aka kama, yana fakewa da cewa don kariya ne, duk da ba su da lasisin mallakar makami, wanda hakan ya saba wa dokar makamai.
Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da bindigogi da dama da aka samu ba bisa ka’ida ba, harsashi hudu na bindigar LAR, da harsashi guda na AK-47. An cafke wadanda ake zargin ne yayin wani samame da aka kai a Karamar Hukumar Tambuwal.
Haka zalika, a ranar 23 ga Afrilu, 2025, jami’an ‘yan sanda daga ofishin Tureta sun tsare wani Yau Lawali daga Kauyen Yabawa a Karamar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara yayin duban ababen hawa. An same shi da bindigogi biyu da aka kera gida da kuma harsasai uku na AK-47.
‘Yan Sanda A Jihar Sokoto Sun Kama Masu Safarar Makamai
