yan Boko Haram sun sace yan mata 15 a jamhuriyar Nijar

Wasu yan bindiga da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne sunyi awon gaba da yan mata 15 a wani kauye dake kusa da garin Toumur a kudu maso gabashin jamhuriyar Nijar a cewar magajin garin, garin

Boukar Mani Toumur magajin garin birnin dake yankin Diffa wanda ya haɗa iyaka da Najeriya ,ya ce kusan yan bindiga su 50 da ba iya gane ko suwaye ba suka sace yan matan a wani kauye dake da tazarar kilomita 9 daga cikin birnin.

A ranar Alhamis ne wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kashe mutane 7 dake aiki a wani kamfanin hakar rijiya na kasar Faransa.

Ya zuwa yanzu babu wani karin haske kan batun sace yan matan.

Ƙungiyar ta Boko Haram ta kara tsaurara hare-haren da take kaiwa a yankunan dake kan iyakar kasashen biyu cikin yan kwanakin nan.

More from this stream

Recomended