
Sojojin Najeriya suna yaki da mayakan Boko Haram a arewacin kasar
Rahotannin sun ce sojoji sun dakile harin, amma an samu asarar rayuka daga dukkan bangarorin.
Wasu mazauna garin na Gudumbali sun ce mayakan sun yi gaba da kayan abinci da kuma makaman soji.
Kawo yanzu dai, rundunar sojin Najeriyar ba ta ce komai ba game da harin.
A watan Yuni ne gwamnatin Najeriyar ta yi kira ga dubban mutanen da suka gudu daga garin na Gudumbali sakamakon hare-haren Boko Haram da su koma gidajensu.