Yan bindiga sun kashe tsohon mataimakin kwantirolan gidajen yari a gonarsa

[ad_1]








Hukumar Kula Da Gidajen Yari A Najeriya, ta tabbatar da mutuwar, Nanvyet Gwali tsohon mataimakin kwantirola a hukumar.

Francis Enabore jami’in hulda da jama’a na hukumar shine ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da yafitar ranar Talata.

Enabore ya ce wasu Æ´anbindiga ne da ba a san ko suwaye ba suka kashe Gwali ranar 10 ga watan Agusta a gonarsa dake Laminga a wajen garin Keffi dake jihar Nasarawa.

Marigayin ya yi sauyin wurin aiki daga ma’aikatar ilimi ta jihar Plataeu ya zuwa hukumar a shekarar 1989 inda ya fara daga mukamin sufuritanda har ya daga ya zuwa mataimakin kwantirola.

Ya yi ritaya daga aiki cikin watan Fabrairun shekarar 2016 a matsayin mataimakin kwantirola mai lura da sha’anin kudi.

Enabore ya ce hukumar na cigaba da tuntubar hukumomin tsaro da abin ya shafa waÉ—anda ke cigaba da bin sahun wadanda suka aikata haka domin tabbatar da cewa sun gurfana gaban sharia.




[ad_2]

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...