‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji Biyu da Wasu Mutane a Ƙaramar Hukumar Apa ta Jihar Benue

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun hallaka mutane huɗu, ciki har da sojoji biyu, a wani hari da suka kai kauyen Ijaha Ikobi da ke ƙaramar hukumar Apa a Jihar Benue.

Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Adakole ya ce maharan, sun kai harin ne a ranar Laraba da misalin ƙarfe 3:30 na rana.

“Mutane sun fara jin karar harbe-harbe a cikin ƙauyen, daga baya kuma wasu sojoji da suka amsa kiran gaggawa suka shiga tarkon da aka shirya musu, inda aka kashe su biyu,” in ji Adakole.

Ya ƙara da cewa sojojin sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin kare mutanen kauyen, kuma maharan sun arce da makamansu. Hakanan ya bayyana sunayen wasu da aka kashe a harin da suka haɗa da Ocheje Ngbede Sani da Aduba Paul Ogboyi.

Shugaban ƙaramar hukumar Apa, Adam Ogwola, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake magana da manema labarai a waya a ranar Alhamis. Ya ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na safiyar Laraba.

More from this stream

Recomended