‘Yan bindiga sun kashe mutum 6 a Zamfara

Jihar Zamfara na yawan fuskantar hare-hare 'yan bindiga

Jihar Zamfara na yawan fuskantar hare-hare ‘yan bindiga

Rundunar ‘yan sanda jihar Zamfara ta ce akalla mutum shida sun rasa rayukansu ciki harda jami’in dan sanda guda a wani harin bindiga da aka kai kauyen Gurbin Baure da ke karamar hukumar Zurmi.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar SP Muhammad Shehu, ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindiga ne da babu adadi suka farwa kauyen a cikin daren Juma’a, inda suka yi ta harbi da kone-kone.

Sai dai a cewar jami’in duk da cewa da farko sun yi kokarin cin karfinsu daga bisani an murkushe su da taimakon jami’an soji.

Mataimakin shugaban karamar hukumar ta zurmi Abubakar Muhammad ya shaidawa BBC cewa mutane na cikin zulumi.

Ya kuma ce gawarwaki takwas suka kidaya da na jami’in dan sanda guda ba shida kamar yadda rundunar ‘yan sanda ke cewa ba.

Kusan shekara guda kenan da ake fuskantar irin wadanan hare-hare a Zurmi duk da matakan da hukumomi da girke jami’an tsaro a yankin da aka ce an yi.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...