’Yan bindiga sun kai hari a kauyen Magaji Wando na jihar Katsina a daren Juma’a, inda suka kashe mutane, suka jikkata wasu tare da yin garkuwa da da dama.
Wani mai sharhi kan tsaro, Bakatsine, ya bayyana a shafinsa na X.
Haka kuma, a ranar Juma’a, ’yan bindiga sun kai farmaki Jabiri community inda suka sace wani matashi tare da yin fashin shanu.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun tsaro sun yi musayar wuta da maharan har suka ja da baya, amma duk da haka sun tsere da wanda suka sace da shanun da suka tafi da su.
’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Tare Da Sace Wasu Da Dama a Katsina
