Aƙalla manoma 27 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a ƙauyen Bindi-Jebbu, wanda ke cikin Tahoss a ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Filato.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa harin ya auku ne da safiyar Litinin, inda maharan suka shiga ƙauyen suna harbe-harbe tare da ƙone gidaje da dama. Hakan ya jawo wasu da dama suka jikkata, inda aka garzaya da su zuwa asibitoci ciki har da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos da Asibitin Filato.
Shugaban ƙaramar hukumar Riyom, Bature Sati Shuwa, ya tabbatar da faruwar harin, sai dai ya ce bai da adadin yawan waɗanda suka mutu a lokacin da ya ke cikin hanyar zuwa yankin.
Hukumomin tsaro da suka haɗa da Operation Safe Haven da rundunar ‘yan sandan jihar, ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da harin har zuwa lokacin da ake wallafa rahoton.
Sai dai shugaban ƙasa na ƙungiyar matasan Berom Youth Moulders Association (BYM), Dalyop Solomon, ya tabbatar wa manema labarai cewa mutane 27 ne suka mutu a harin.
‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 27 a Sabon Hari a Riyom, Jihar Filato
