‘Yan Bindiga Sun Kashe Jariri Dan Kwana Uku, Sun Kuma Sace Mahaifiyarsa a Katsina

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari da daddare a kauyen Zagami da ke yankin mazabar Yankara a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, inda suka hallaka mutane da dama tare da sace wasu, ciki har da mata da yara.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya auku ne da misalin karfe takwas na dare a ranar Laraba, inda maharan suka kutsa cikin kauyen tare da buda wuta ba tare da kakkautawa ba.

Wani masani kan harkokin tsaro mai suna Bakatsine, ya bayyana a dandalin X a ranar Alhamis cewa lamarin ya kasance mummunan abu da ya girgiza al’umma.

A cewarsa, “Wani jariri dan kwana uku ya rasa ransa a yayin harin, inda kuma aka sace mahaifiyarsa.”

Duk da cewa ba a bayyana adadin mutanen da aka kashe ko aka sace ba, mazauna yankin sun bayyana harin a matsayin daya daga cikin mafi muni da suka fuskanta a cikin makonnin baya-bayan nan.

Hukuma ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da harin, sai dai jama’a na kira da a dauki matakin gaggawa domin hana sake afkuwar irin wannan hari a yankin.

More from this stream

Recomended