‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Al’ummar Yan Shuni, Sun Sace Mutane a Jihar Katsina

A daren Lahadi, ‘yan bindiga sun kai hari a Yan Shuni da ke Jihar Katsina, inda suka jikkata mutum guda, suka sace wasu mazauna garin da dama, tare da yin awon gaba da dabbobi masu tarin yawa.

Wani mai nazari kan harkokin tsaro, Bakatsine, ne ya bayyana faruwar lamarin a shafinsa na X a ranar Litinin.

“‘Yan bindiga sun kai hari a al’ummar Yan Shuni jiya da daddare, sun jikkata mutum guda, sun sace mutane da dama, kuma sun tafi da dabbobi masu yawa,” in ji shi.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a tantance adadin mutanen da aka sace ba.

Al’ummar Yan Shuni, kamar sauran yankunan karkara a Jihar Katsina, na fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga akai-akai.

Hukumomi dai har yanzu ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.

More from this stream

Recomended