Kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC) ta bayyana cewa sama da mutane miliyan 3.7 ke fama da matsananciyar yunwa a jihohin Borno, Adamawa da Yobe sakamakon rikicin da ya durƙusar da kasuwanci da hanyoyin samun aiki.
ICRC ta ce tana taimakawa sama da iyalai 21,000 da iri da kayan aikin noma, tare da shirin raba famfunan ban-ruwa da hasken rana domin noman rani.
A cewar shugaban ofishin ICRC a Maiduguri, Diana Japaridze, akwai fargabar karancin abinci daga watan Yuli zuwa Satumba.
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa suna yin nisa don nemo itace ko yin noma, yayin da wasu iyalai ke kwana da yunwa har na tsawon kwanaki.
Yadda Yunwa Ke Kara Kamari a Arewa Maso Gabashin Najeriya—ICRC
