A ranar Lahadi da ta gabata, wani mummunan lamari ya faru a wurin tace ruwan sha na Gubi Dam da ke ƙarƙashin Hukumar Samar da Ruwa ta Bauchi, inda ma’aikata hudu suka rasu yayin da suke tsaftace wurin.
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu har da mahaifi da ɗansa.
Wani ma’aikacin hukumar ya shaida
cewa biyu daga cikin waɗanda suka rasu ma’aikata ne na dindindin, yayin da sauran biyun ’yan kwangila ne.
“Lamarin ya faru ne a yayin da suke tsaftace wurin tace ruwa da ke baiwa birnin Bauchi ruwa. Sun shiga cikin rijiyar ajiye ruwa inda suka ga kifaye suna iyo. Daya daga cikinsu ya yi yunkurin kamawa, sai ya nutse. Na biyu ya bi shi domin cetonsa, shi ma ya nutse. Haka har na uku da na hudu suka shiga domin ceto juna, amma dukkansu suka rasu,” inji wani ma’aikacin da ya nemi a sakaya sunansa.
Wadanda suka mutu su ne: Ibrahim Musa, Shu’aibu Hamza, Jamilu Yunusa, da Abdulmalik Ibrahim Hamza. An binne su nan take a ranar Lahadin.
Wani daga cikin mamatan, kamar yadda rahotanni suka nuna, yana shirin yin aure ne kafin afkuwar wannan mummunan lamari.
Yadda Wani Mahaifi da Ɗansa da Wasu Mutum 2 Suka Rasa Rayukansu a Bauchi
