Yadda wani adalin direba ya kawo cigiyar haka maƙare a kuɗi

Wani direban motar kasuwa ya mayarwa rundunar ‘yan sandan jihar Kano jakar da ta bata dauke da makudan kudade.
 
Direban mai suna Safiyanu Mohammed dan shekara 36 yana zaune ne a unguwar Rangaza Quarters da ke karamar hukumar Ungogo a jihar Kano.

Ya tsinci jakar ne a ranar Juma’a 9 ga watan Agusta 2024 a titin Hadejia kusa da mahadar Dakata, sannan ya kai ga hukumar ‘yan sanda. 

An gano jakar na dauke da makudan kudade, amma babu wani takamaiman shaida ko bayanan tuntuɓar mai shi.
 
Yanzu haka dai rundunar ‘yan sandan jihar Kano tana kira ga wanda ya mallaki wannan haka da ya fito ya karbi dukiyarsa. 

Don sauƙaƙe dawo da jakar, ana buƙatar mai shi ya ba da shaidar mallaka da ganewa.
 
Kwamishinan ‘yan sanda, CP Salman Dogo Garba, ya yabawa direban bisa ga gaskiya da ya nuna, ya kuma bukaci duk wanda ke da bayanin asalin mai jakar da ya fito.

More from this stream

Recomended