Wasu ‘yan Somaliya sun fara tara kudi ga iyalan wani mutum da aka kona shi har lahira kan batun auren dan dan’uwansa da mata daga wata kabila daban.
Ahmed Mukhtar Salah dai kawun wannan mai neman auren ne wanda dan kabilar Bantu ne, da ya je ya yi baiko da wata mace ‘yar wata babbar kabila a asirce.
Iyayen yarinyar sun tursasawa Mista Ahmed cewa ya nemo wannan yarinya, bayan da suka farga cewa dan dan’uwan nasa ya gudu da ita.
Wakilin BBC Ibrahim Aden ya ce daga baya dai mahaifin yarinyar ya amince ya sanyawa ma’auratan albarka, amma mahaifiyarta da sauran dangi sun ki yarda su yi hakan.
A makon da ya gabata ne aka caka wa Mista Ahmed wuka aka kuma kona shi da ransa inda ya mutu a Mogadishu, babban birnin kasar.
Tuni dai ‘yan sanda suka kama mahaifiyar yarinyar da kuma wasu mutanen da suke da hannu kan wannan aiki.
Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa jama’a da dama sun taru a wajen jana’izar Mista Ahmed da aka yi a ranar Lahadi.