
Nnamdi Kanu jagoran kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra bayyana yadda ya tsere lokacin da sojoji suka yi dirar mikiya a gidan mahaifinsa.
A wata tattaunawa da wani gidan talabijin mai suna TV Channel 1 na kasar Isra’ila Kanu ya bayyana cewa da taimakon yan uwa aka yi fasa kwaurinsa zuwa wajen Najeriya.
Jagoran fafutukar ya bace tun lokacin da rundunar Sojan Najeriya dake gudanar da atisayen da a kai wa lakabi ‘Operation Phython Dance’ suka kai masa farmaki biyo bayan takalarsu da yan kungiyar suka yi.
Ya yin da aka haramta kungiyar, Kanu ya bace tun daga wancan lokaci sai a yan kwanakin nan ya bayyana a wani bidiyo da ya nuna shi yana gabatar da ibada a birnin Jerusalem na kasar Isra’ila.
A tattaunawar Kanu ya bayyana cewa mutane 28 aka kashe lokacin da sojojin suka kai farmakin.
Kanu ya ce mutanensa ne suka dauke shi kafin sojojin su karasa dakin da yake inda daga bisani kuma suka fice da shi daga Najeriya.