Wata Kungiya Ta Nemi Gwamnan Zamfara Da Ya Yi Murabus Saboda Matsalar Tsaro

Wata kungiya mai suna Coalition for Good Governance and Accountability in the North-West (COGGAN), wacce ke fafutukar inganta shugabanci a yankin Arewa maso Yamma, ta bukaci Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da ya ajiye mukaminsa saboda gaza cika alkawuran da ya dauka a lokacin kamfen, musamman na yaki da matsalar tsaro da kuma inganta ilimin boko.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Talata mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Alhaji Ibrahim Anka, ta ce gwamnatin Lawal ta gaza faranta wa jama’a rai tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.

COGGAN ta tunatar da cewa a lokacin yakin neman zabe na 2023, Gwamna Lawal ya sha alwashin kawo karshen matsalar ‘yan bindiga cikin watanni uku da haukarsa mulki, amma yanzu sama da shekara guda kenan da zama kan karagar mulki, amma matsalar tsaro na ci gaba da ta’azzara a sassa daban-daban na jihar.

Kungiyar ta bayyana damuwarta kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da jefa al’umma cikin tsoro, tare da hana manoma zuwa gonaki, da kuma durkusar da kasuwanni da harkar ilimi, lamarin da ya haifar da kunci ga rayuwar jama’a.

Dangane da ilimi kuwa, COGGAN ta soki yadda gwamnatin ke tafiyar da wannan fanni, tana mai cewa har yanzu jihar na fama da karancin ingantattun makarantun firamare da kuma rashin kayan aiki da yanayi mai kyau na koyarwa.

More from this stream

Recomended