
Wasu daga cikin yan majalisar kasa ya’yan jam’iyyar APC dana PDP sun bawa hammata iska lokacin da shugaban kasa Muhammad Buhari ke gabatar da kasafin kudin shekarar 2019.
Rikicin ya fara ne bayan da wasu yan majalisar da suka fito daga jam’iyar APC suka yi kokarin kwace kwalayen da abokan aikinsu na jam’iyar PDP suka zo da shi.
Yan majalisar na jam’iyar PDP sun shirya yin amfani da kwalaye masu ɗauke da rubutu domin nuna adawarsu ga shugaban.
Wasu daga cikin kwalayen na dauke da rubutun “Yanci yana samuwa ne ta hanyar jajircewa.”