Wasu matasa sun ƙone ofishin ƴansanda kan kisan wani dalibin jami’a

[ad_1]








Wasu matasa da suka fusata sun ƙone ginin ofishin ƴansanda na Iwo a jihar Osun da safiyar ranar Juma’a.

Matasan sun aikata haka ne bayan da aka kashe wani matashin dalibi mai suna, Tunde Nafiu. Jami’an ƴansanda dake yaki da aikata fashi da makami wato SARS sune suka bude wuta akan matashin.

An harbe Nafiu lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Olupono wani gari dake kusa da su a ranar Alhamis.

Matasan da suka fusata sun fantsama kan tituna suna zanga-zanga inda suka kona caji ofis ɗin ƴansandan.

Da yake magana kan abinda ya faru kwamishinan ƴansandan jihar, Fimihan Adeoye ya ce har yanzu ba a gano musabbabin harbin da ya kai ga mutuwar dalibin ba

Adeoye ya kara da cewa ƴansanda hudu dake sintiri lokacin da abin yafaru na can a kulle ya kara da cewa idan har an same su da laifi to za su fuskanci shari’a.




[ad_2]

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...