Wasu masu garkuwa da mutane sun faɗa hannun ƴan sanda a Kaduna

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wasu gawurtattun masu garkuwa da mutane su 4 da suka shahara  wajen yin garkuwa da mutane a yankin arewa maso yamma.

Bindiga  ƙirar AK-47 da kuma wata ƙaramar bindiga ƙirar gida aka gano daga wurin masu garkuwar.

A wata sanarwa da rundunar ƴan sandan jihar ta fitar mai magana da yawun rundunar ASP Mansir Hassan ya bayyana cewa a ranar 29 ga watan Mayu bisa dogaro da bayanan sirri da wani ɗan kasa nagari ya kwarmata musu haɗin gwiwar sintirin jami’an tsaro daga ofishin ƴan sanda na Saminaka da kuma ƙungiyar mafarauta dake ƙaramar hukumar Lere suka samu nasarar kama masu garkuwa da mutane da kuma satar shanu su uku.

Mai magana da yawun rundunar ya ce waɗanda aka kama sun haɗa da Isah Baffa Rabo mai shekaru 30 daga ƙauyen Maibindiga a ƙaramar hukumar Lere wanda yake da hannu a yin garkuwa da mutane a ƙananan hukumomin Zangon Kataf da Kachia dake jihar, Jafaru Saleh mai shekaru 30 da kuma Umar Musa mai shekaru 24 dukkansu sun fito daga ƙauyen Durimi dake Lere.

Mutanen sun amsa laifin yin garkuwa da mutane da kuma satar shanu biyu da suka sayarwa da wani Idris Abubakar da shima ya faɗa hannun jami’an tsaro.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...