Wani matashi mai shekaru 24 ya hallaka kansa bayan shan tabar wiwi

[ad_1]








Rundunar ƴansandan jihar Enugu ta fara bincike kan lamarin da yakai ga mutuwar wani matashi mai shekaru 24 baya da sha ganyen tabar wiwi fiye da ka’ida.

Mai magana da yawun rundunar, SP. Ebere Amaraizu, shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa, jiya a Enugu.

Ya ce lamarin yafaru ne ranar 22 ga watan Agusta a kauyen Ameke dake karamar hukumar Aninri ta jihar Enugu.Amaraizu ya bayyana wanda ya mutu da suna,Ebube Chukwu.

Ya ce an rawaito cewa Chukwu ya kashe kansa bayan da ya sha ganyen tabar wiwin da akafi sani da Igbo

“An rawaito cewa marigayin ya rataye kansa a saman wata bishiya dake cikin dajin Obokolo,”ya ce.

“An kuma gano cewa mamacin na da dabi’ar shan tabar wiwi a koda yaushe wacce za ta iya jawo aikata mummunan lamarin.”




[ad_2]

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...