Shekara guda bayan rushewar Gadar Namnai da ke kan hanyar Jalingo-Wukari a Jihar Taraba, Gwamnatin Tarayya na fuskantar suka daga bangarori da dama bisa abinda ake kallo a matsayin sakaci da gazawa wajen gyaran wannan muhimmin gini.
Gadar, wadda ke kan hanyar tarayya da ke hade jihohin Benue, Taraba da Adamawa, na ci gaba da kasancewa cikin lalacewa ba tare da wani aiki na gyara ba, lamarin da ya tilastawa fasinjoji, ‘yan kasuwa da dalibai amfani da kwale-kwalen da ke da hadari domin ketarewa.
Duk da cewa hanyar na da matukar muhimmanci wajen hada yankin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas da kuma Arewa maso Yamma, babu wani yunkuri da aka fara na gyara gadar da ta karye.
A wata sanarwa da ya fitar a Jalingo, babban birnin Taraba, a ranar Laraba, fitaccen malamin jami’a, Farfesa John Ajai, ya bayyana irin matsin da ya shiga yayin da yake kokarin wucewa ta hanyar makarewar da gadar ta haddasa a makon da ya gabata.
“Jirgin ruwa da muke ciki ta makale a cikin yashi. Ba mu iya sauka ba. Dole aka fara kwashe fasinjoji cikin firgici da rashin tsaro. Motocin da ke cikin kwale-kwalen sun makale sama da rabin sa’a. Sai dai rahamar Allah ne kadai ya hana afkuwar wani mummunan hadari,” in ji shi.
Farfesan ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abin da ba wai kawai yana takura ba ne, har ma yana jefa rayukan mutane cikin hadari a kullum, kana yana janyo tsaiko ga harkokin tattalin arziki da zamantakewa a yankin.
Ya soki shiru da halin ko-in-kula da Gwamnatin Tarayya ke nunawa kan wannan matsala, yana mai cewa hakan na nuni da “gazawar gudanar da hakkin kasa.” Ya kara da cewa har yanzu babu wani bayyani daga Ma’aikatar Ayyuka ko Hukumar Kula da Hanyoyin Tarayya (FERMA) kan yadda za a magance matsalar—ba a tura kwangiloli ba, kuma babu wani lokaci da aka kayyade na kammala aikin.
Haka kuma, Farfesa Ajai ya bukaci ‘yan majalisar tarayya daga Taraba su daina yin shiru su matsa lamba wajen ganin an kawo dauki cikin gaggawa.
“Ko da ba ku da ikon gudanar da ayyukan tarayya kai tsaye,” in ji shi, “amma muryoyinku na da matukar muhimmanci. Shiru naku yana nufin yarda da abin da ke faruwa.”
A karshe, ya tambaya ko wannan sakaci zai faru ne idan gadar na Abuja ko Legas ce, yana mai bukatar a duba batun da gaggawa da kulawa ta musamman.
Wani Malamin Jami’a Ya Caccaki Gwamnatin Tarayya Kan Gazawa Wajen Gyaran Gadar Da Ta Rufe Hanya a Taraba
