Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta biya dukkan basussukan da gwamnatocin da suka gabace ta suka bari na biyan kuɗin jarabawa ga hukumomin WAEC da NECO, wanda hakan ya sa an saki sakamakon ɗaliban da aka riƙe tsawon shekaru.
Wani jawabi daga mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa sakamakon jarabawarm WAEC da NECO daga shekarar 2018 zuwa 2022 yanzu haka an sake su bayan an biya bashin da ake bin gwamnatin jihar.
“Gwamna Dauda Lawal na nuna cikakken ƙuduri wajen gyara fannin ilimi a jihar. Wannan dalili ne ya sa tun a watan Nuwamban 2023 ya ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi, kuma hakan yana fara haifar da ɗa mai ido,” in ji sanarwar.
Tun daga lokacin, fiye da makarantu 500 aka gyara tare da samar musu da kayan aiki, haka kuma malamai na karɓar horo da sake horarwa a jihar.
Gwamnatin baya ta kasa biyan kuɗin jarabawar WAEC daga shekarar 2018 zuwa 2022, inda aka bar bashin Naira biliyan 1.4, wanda yanzu gwamna Lawal ya biya gaba ɗaya. Saboda rashin biyan kuɗin 2023, babu wata makarantar gwamnati a jihar da ta shiga jarabawar WAEC a wancan shekarar, amma a bana an biya kuma ɗalibai sun rubuta jarabawar.
A ɓangaren NECO, gwamnati ta biya Naira miliyan 320 domin biyan bashin da ake bin su daga shekarar 2020 zuwa 2021. Bugu da ƙari, gwamnati ta amince da biyan bashin da NECO ke bi daga shekarar 2014 zuwa 2018 wanda ya kai Naira biliyan 1.022, wanda shine dalilin da yasa NECO ta riƙe sakamakon ɗalibai na wancan lokaci.
An cimma matsaya da hukumar NECO cewa za ta saki sakamakon da zarar ta karɓi ɓangare na farko na biyan kuɗin.
Wannan mataki na gwamnatin Zamfara na ɗaya daga cikin kokarin gyara fannin ilimi da kawo sauƙi ga ɗalibai da iyayensu a jihar.
WAEC da NECO sun saki sakamakon jarabawar ɗaliban Zamfara da aka jima ana riƙe da shi
