Tsugunne ba ta kare ba a jam’iyyar PDP a Kano

Tambarin jam'iyyar PDP

Tsugunne ba ta kare ba a game da wanda zai tsaya wa jam’iyyar PDP takarar gwamna a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.

Bayan zaben fitar da gwanin da jam’iyyar ta PDP a jihar da ake ganin na yi wa tsohon gwamnan jihar Rabi’u Musa Kwankwaso biyayya, tare da fitar da Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamna, sai ga shi wasu bayanan na cewa uwar jam’iyyar ta tattaro shugabannin jam’iyyar na jihar tare da yin taro, inda ta tsayar da Malam Salihu Sagir Takai a matsayin dan takarar gwamna.

Wanda aka tsayar mataimakin gwamnan, Kwamared Aminu Abdulsalam, ya shaida wa BBC cewa zancen tsayar da dan takara bayan na su, zance ne na kanzon kurege.

Ya ce ‘ Har yanzu akwai mutanen da ke ta kai ruwa rana a jihar, saboda ba su ci zaben ba, kuma suna ganin cewa lallai sai abin da suke so za a yi musu.’

Kwamared Aminu Abdulsalam, ya ce ba yadda za a yi ace an yi taro da wakilan jam’iyya na jiha da na kasa, sannan kwamitin da aka tura domin su gudanar da zabe sun zo jihar Kano sun gudanar da zabe, kuma hukumar zabe ta kasa reshen jiha ta halarci taron ta kuma shaida abin da aka yi, sannan wani daga baya yazo ya ce ba ayi zabe ba.

Ya ce zaman da ake ce an yi inda aka bayyana wani dan takara daban, ba ayi da su ba, kuma ba ayi da kowa ma face su masu cewa ba su yarda da Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamna ba.

Dan takarar mataimakin gwamnan ya ce ‘ Jam’iyyar PDP ai ba ta su bace su kadai, sannan kuma ai ba a yin zaben dan takarar Kano a Abuja,dan takarar Kano a Kano ake yi, kuma hasali ma lokacin zabe ya wuce’.

Ya ce batun cewa wai ba a gudanar da zaben fitar da gwani ba a wasu kananan hukumomin jihar ba, to zaben da aka yi an yi shi a gaban mutane da kuma kamarar daukar hoto, sannan an yi shi a dukkan kananan hukumomin Kano 44, hasali ma suna da kaset cikakke na yadda aka gudanar da zaben.

More from this stream

Recomended