Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki kuma ya koma jam’iyyar SDP.
Bayanai sun nuna cewa ya riga ya mika takardar murabus dinsa ga shugabancin APC a mazabarsa da ke Kaduna. Haka kuma, ya bukaci magoya bayansa da na hannun damansa su mara masa baya zuwa SDP.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa ranar Litinin, 10 ga Maris, 2025, El-Rufai ya caccaki shugabancin APC, yana mai zargin jam’iyyar da watsi da manyan manufofin da aka kafa ta a kai.
El-Rufai ya bayyana cewa ya dade yana nuna damuwa kan yadda APC ke tafiya, amma ba a dauki matakin gyara ba. Ya kuma tunatar da irin rawar da ya taka wajen kafa jam’iyyar a 2013 da kuma nasarorin da jam’iyyar ta samu a zaben 2015, 2019, da 2023.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa a Kaduna ta mayar da hankali kan ilimi, kiwon lafiya, ginshikan rayuwa, da samar da ayyukan yi, amma ya koka cewa APC a yau ba ta cika alkawuran da ta dauka ga ‘yan Najeriya.
Sauya shekarsa zuwa SDP na iya yin tasiri matuka a siyasar Arewacin Najeriya, musamman duba da irin tasirin da yake da shi a yankin.
Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai Ya Fice Daga APC, Ya Koma SDP
