Tsadar rayuwa: Tinubu zai gana da gwamnoni

A yau Alhamis ne shugaban kasa Bola Tinubu zai yi wata ganawar sirri da gwamnonin jihohi a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja, domin samar da hanyoyin magance tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Ana sa ran gudanar da taron kafin tafiyar shugaban kasar zuwa kasar Habasha domin halartar taron kungiyar tarayyar Afrika.

Wannan na zuwa ne dai a daidai lokacin da rayuwa ta yi masifar tsada inda har a wasu yankunan ƙasar aka fara gudanar da zanga-zanga.

More from this stream

Recomended