Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya a yau, Laraba, domin wata gajeriyar ziyarar aiki a birnin Paris na ƙasar Faransa.
Mataimakinsa na musamman kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja.
Sanarwar ta ce yayin ziyarar, Tinubu zai duba yadda gwamnatinsa ta gudanar da mulki a tsakiyar zangon wa’adinsa, tare da nazarin manyan nasarorin da aka cimma.
Haka nan, shugaban zai yi amfani da wannan lokaci don tantance cigaban da aka samu a kan sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa, tare da tsara dabaru domin tabbatar da ci gaba a shekara mai zuwa.
Tinubu Zai Tafi Faransa Don Ziyarar Aiki
