Tinubu ya sanya hannu kan dokar mafi ƙarancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar gyara mafi karancin albashi na kasa na 2024 ta zama doka.

Dokar dai za a sake duba ta duk shekara uku.

Hakan ya biyo bayan kudurin da gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin kwadago suka yi na biyan mafi karancin albashi na N70,000.

Tinubu ya sanya hannu ne a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin bayan da majalisar dokokin kasar ta amince da kudirin.

Shugaban ya rattaba hannu kan kudirin dokar a tsakiyar zaman majalisar zartarwa ta tarayya.

Shugaban ma’aikatan gwamnati ya ce babu shakka sabuwar dokar za ta tabbatar wa ma’aikata cewa shugaban ya damu da jin dadin su.

More News

An yi garkuwa da wasu mutum 11 ƴan gida ɗaya

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan gida daya mutum 11 da suka hada da mata da ‘ya’yan wani dan jarida mazaunin...

Matsin rayuwa ya sa wani ɗansandan Najeriya ya halaka kansa

Wani Sufeto Dasu Kassa ya rasu a jihar Adamawa.  Rahotanni sun bayyana cewa, an tsinci Kassa a gidansa da ke Anguwan Yungur a karamar...

Ƴan ta’adda sama da 260 sun miƙa wuya ga jami’an tsaro

Yayin da dakarun Operation Lake Sanity 2 ke kara kai hare-hare, rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) ta yi nasarar karɓar...

Ƴan sanda sun kama masu safarar makamai wa ƴan bindiga

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Karasuwa a jihar Yobe sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai da...