Theresa May ta iso Najeriya inda take ganawa da Buhari a Aso Rock

[ad_1]








Firaministan Birtaniya, Theresa May ta iso Najeriya.

Da isowarta May ta wuce fadar shugaban kasa inda yake ganawa da shugaban kasa, Muhammad Buhari.

Firaministan ta samu tarba daga shugaban kasa Muhammad Buhari tare da wasu daga cikin ministocinsa.

Ziyarar May zuwa Najeriya wani ɓangare ne na ziyarar da take wasu ƙasashen Afirka uku.Ta ziyarci kasar Afirka ta Kudu a jiya Talata kana ta wuce kasar Kenya daga Najeriya.

Ya yin da take Najeriya May za ta tattauna da shugaban kasa Muhammad Buhari kan matsalar tsaro da ta addabi kasar, tattalin arziki da kuma kulla yarjejeniyar kan tsaro da kuma tattalin arziki.

Da take magana a birni Cape Town na kasar Afirka ta kudu May ta bayyana Æ´an Najeriya miliyan 87 ne ke rayuwa cikin talauci.




[ad_2]

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...