Theresa May na gab da isowa Nigeria

[ad_1]

Theresa May

Image caption

Misis May ta faro ziyarar daga kasar Afirka ta Kudu. daga Najeriya kuma za ta wuce kasr Kenya

Firai ministar Birtaniya Theresa May za ta taso daga birnin Cape Town na Afirka ta Kudu, zuwa Najeriya a rana ta biyu a ziyarar da ta ke yi nahiyar Afirka.

Za dai ta gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja ,wannan ne karo na farko da firaministan Burtaniya zai ziyarci Najeriya cikin shekara 7.

Theresa May tana ziyarar ne tare da wata tawagar ‘yan kasuwa, inda kuma za a tattauna batutuwna da suka shafi huldar cinikayya tsakanin Birtaniya da Afirka, musamman ma a lokacin da Birtaniya ke gab da ficewa daga Tarayyar Turai.

Dangantakar Burtaniya da kasashen Afirka, musamman ma Najeriya bayan ficewar Burtaniya din daga tarayyar Turai na daga cikin muhimman abubuwan da ake tunanin ziyarar za ta mamaye musamman ganawar da za a yi tsakanin ta da shugaba Buhari.

Ana sa ran shugabannin za su tattaun kan batun tsaro, da safarar mutane da kasuwanci, da duba hanyoyin ci gaban mulkin demokradiyya, da karfin huldodi na tattalin arziki da cinikayya, da kuma magance matsaloliln tsaro, musaman ma ta’addanci a yayin da birtaniya ke shirin fita daga Tarayyar Turai.

Jakadan Birtaniya a Najeriya Paul Thomas Arkwright ya shaida wa manema labarai a Abuja gabanin isowar firaminista cewa Birtaniya na duban wasu yankuna baya ga kasashen Turai a shirinta na ficewa daga tarayyar turai, tana duba sauraran yankuna na duniya.

Ana sa ran kara dankon dangantaka, ba wai da kasashen da aka saba da su ba irin Najeriya kawai, har ma da wasu kasashen na daban tare da duba yadda za a karu da juna, tare da magance barazanar da duniya ke fuskanta musamman a Afirka da kuma Birtaniya.

Birtaniya ita ce kasa ta biyu a karfin zuba jari a Afirka, kuma ana ganin Misis May za ta yi amfani da ziyarar ne domin kokarin inganta huldar tsakanin kasarta da kasashen Afirka.

Daga Abuja za ta wuce birnin Lagos dan ganawa da mutanen da suka samu kansu a cikin bautar bayi a zamnance.

Za dai ta gabatar da wasu matakai da ya kamata a dauka dan taimakawa Nigeria da Nijar tsare iyakokinsu, a kokarin magance kwararar ‘yan ciranin yammacin Afirka dan isa nahiyar turai.

Nigeria dai ita ce ta biyu a nahiyar Afirka cikin abokan huldar kasuwancin Birtaniya kasar da ta mulketa.

[ad_2]

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...