Sufeto Janar Na ‘Yan Sanda Zai Tattauna Da Tsofaffin Jami’an ‘Yan Sanda Da Ke Zanga-Zanga Kan Hakkokinsu


Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana aniyarsa ta ganawa da tsofaffin jami’an ‘yan sanda da suka fito zanga-zanga a Abuja domin neman gyaran hakkokinsu na fansho.

Kwamishinan ‘yan sanda na Babban Birnin Tarayya ne ya isar da wannan sakon a madadin Sufeton Janar.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana a wani sakon da ta wallafa a shafinta na X cewa Kwamishinan ya gana da masu zanga-zangar, kuma an shirya wa Sufeton Janar ganawa da su a dakin Peacekeeping da ke Hedikwatar Rundunar a Abuja.

An gudanar da zanga-zangar ne karkashin jagorancin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC) a 2023, Omoyele Sowore, domin neman ingantaccen walwala ga jami’an ‘yan sanda da suka yi ritaya da kuma wadanda ke bakin aiki.

Rundunar ta kara da cewa “wasu da ke da wata manufa ta daban sun yi yunkurin karkatar da zanga-zangar,” ba tare da bayar da cikakken bayani a kai ba.

More from this stream

Recomended