Sojojin Najeriya Sun Lalata Wuraren Tace Man Fetur 12 a Yankin Neja Delta

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun lalata wurare 12 da ake tace man fetur ba bisa ƙa’ida ba a yankin Neja Delta da ke kudancin ƙasar.

Cikin wata sanarwa da muƙaddashin daraktan yaɗa labaran runduna ta 6 ta sojin Najeriya da ke birnin Fatakwal, Laftanar Kanal Jonah Danjuma, ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa dakarun sun kuma ƙwato lita 70,000 na man fetur.

A cewar sanarwar, sojojin tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro sun kaddamar da farmaki na mako guda wanda ya kai ga lalata ƙananan jiragen ruwa guda shida da kuma ƙwato bututun mai tara da aka sace. Haka kuma an kama mutane 16 da ake zargi da hannu a ayyukan haramtattun tace mai a jihohin yankin huɗu.

Sanarwar ta kara da cewa farmakin ya gudana daga ranar 27 ga watan Janairu zuwa 2 ga watan Fabrairu, 2025.

More from this stream

Recomended