Sojojin Najeriya sun kwato wasu kauyuka 8 a Borno

Makaman Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta yi ikirarin kakkabe ‘yan Boko Haram a wasu kauyuka da dama a jihar Borno.

Sanarwar da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce samamen da rundunar hadin guiwa ta 25 a Chibok da ta 28 a Damboa suka kaddamar a Gumsari da Gambori a jihar Borno sun yi nasarar kakkabe ‘yan Boko Haram a kauyuka kamar Litawa da Kashmiri da Dole da Mulimari da Mudachira da Njaba da Bale da Gambori

Sanarwar ta ce rundunonin sun kaddamar da farmakin ne a cikin dare a ranar Juma’a.

A cewar sanarwar, sun yi wa ‘yan Boko Haram shigar ba-zata, inda mayakan suka gudu.

Sai dai sanarwar ba ta fadi ko akwai wasu daga cikin mayakan da aka kashe ba a gumurzun, amma ta bayyana cewa mayakan sun gudu sun bar kayayyakinsu da suka hada da keke 17 da wayoyin salula da jarkar fetir da abinci da kayan kwanciya da sauransu.

Duk da ikirarin rundunar sojin Najeriya na karya lagon karfin Boko Haram, amma har yanzu kungiyar na ci gaba da zama barazana a yankin arewa maso gabashi, inda a kwana rahotanni suka ce wasu mahara da ke tunanin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari a garin Katarko a jihar Yobe inda suka kori mutanen gari tare da kone gidaje.

More from this stream

Recomended