A wani sabon mataki na yaki da ‘yan ta’adda, sojojin Najeriya sun kaddamar da samame a jihohin Sokoto da Zamfara, karkashin shirin Operation FANSAN YANMA Phase V, inda suka lalata sansanonin ‘yan ta’adda tare da kwato makamai da wasu kayayyaki na yaki.
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sun mamaye wurare masu hadari kamar Gidan Madi, kauyen Tsamiya, Tudun Ruwa, Alela da kuma dajin Goboro – daya daga cikin wuraren da ake kyautata zaton mafakar ‘yan ta’adda ne a yankin.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa dakarun sun gamu da tsananin adawa daga kungiyar Lakurawa, wacce aka fi sani da kisan gilla da hare-haren kwanton bauna a arewa maso yammacin Najeriya. Sai dai duk da haka, an samu nasarar kwace wasu wurare kamar Areo, Damoria da kauyen Tumuna.
“Wadannan sansanonin na ‘yan ta’adda na taka muhimmiyar rawa wajen kai hari kan fararen hula da jami’an tsaro,” in ji wani babban jami’in soja.
A yayin farmakin, an kashe ‘yan ta’adda guda shida, yayin da wasu suka tsere da harbin bindiga a jikinsu. Jami’in soja guda daya ya jikkata kuma an kai shi asibitin sojoji na rundunar Divishan ta 8 a Sokoto. Har ila yau, wani dan banga da ke taimakawa dakarun soji ya rasa ransa a yayin da yake bakin aiki.
Sojojin sun kwato makamai, harsasai, rediyo biyu na hannu da babura da ake amfani da su wajen kai farmaki da sadarwa tsakanin ‘yan ta’addan.
Sojojin Najeriya sun kai farmaki kan sansanonin ‘yan ta’adda a Sokoto da Zamfara, sun kashe wasu, sun kwato makamai
