Sojojin Sector 2 na Rundunar Sojin Najeriya, tare da hadin gwiwar Jiragen Yaki na Operation Fasan Yamma (OPFY), sun kubutar da mutane 101 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Kankara na Jihar Katsina da kuma Shinkafi a Zamfara.
Kakakin OPFY, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ya bayyana cewa a yayin wannan farmaki, sojojin sun kashe ‘yan ta’adda 10 a fafatawar da suka yi a yankin Faru, karamar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.
A cikin wata sanarwa da Hukumar Hadin Kai ta Yada Labarai ta OPFY ta fitar, an bayyana cewa sojojin sun kai farmaki a sansanin ‘yan ta’adda da ke Pauwa High Ground a Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina, inda suka kashe ‘yan bindiga uku tare da ceto mutane 84.
Bayan haka, an mika wadanda aka ceto ga hukumomin kananan hukumomi don ci gaba da daukar matakin da ya dace.
Har ila yau, an ceto wasu mutane 17 da wani shahararren shugaban ‘yan bindiga ya yi garkuwa da su a kauyukan Tsibiri da Doka da ke cikin Karamar Hukumar Shinkafi. A halin yanzu suna karbar kulawar lafiya a wani asibiti a yankin.
Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 10, Sun Ceto Mutane 101 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Katsina Da Zamfara
