Sojojin Najeriya da ke karkashin rundunar Operation Hadin Kai sun samu wata nasara a kokarinsu na kakkabe ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas, inda suka kashe ‘yan Boko Haram guda biyar a wani samame da suka kai a yankin Ladin Buttu na dajin Sambisa.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun gamu da ‘yan ta’addan ne a yayin wani atisayen sintiri da suke gudanarwa, inda suka gwabza fada mai tsanani. Bayan musayar wuta, sojojin sun kashe mutane biyar daga cikin ‘yan ta’addan, yayin da wasu suka tsere da raunuka.
Bayan kammala aikin, sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku, da makaman harsasai guda biyar da sauran kayan yaki da ake kyautata zaton za a yi amfani da su wajen kai farmaki a gaba.
Wannan nasara na daga cikin sabbin matakan rundunar sojin Najeriya wajen dakile ayyukan ta’addanci, musamman bayan umarnin da Babban Hafsan Sojin Kasa ya bayar na kara zafafa hare-haren kasa da na sama a cikin dazukan da ‘yan ta’addan ke buya.
Rahoton ya kara da cewa dakarun sun fadada ayyukansu zuwa wasu sassa na dajin Sambisa, yankin Timbuktu Triangle da kuma iyakokin tafkin Chadi, da nufin murkushe dakarun Boko Haram da ISWAP baki daya.
Rundunar sojin Najeriya ta jaddada kudirinta na ci gaba da matsa lamba har sai an dawo da cikakken zaman lafiya a yankunan da rikici ya shafa.
Sojojin Najeriya sun hallaka mayaƙan ‘yan BH biyar a Sambisa, sun kuna ƙwato makamai
