Sojojin Najeriya Sun Dakile Harin Boko Haram a Sansanin Soja a Adamawa

Dakarun haɗin gwiwa na sojojin Najeriya sun yi nasarar dakile wani harin Boko Haram da aka kai kan sansanin soja da ke ƙauyen Waga, a ƙaramar hukumar Madagali, Jihar Adamawa.

Wani masani kan tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ce majiyoyin leƙen asiri sun sanar da shi cewa harin ya faru da misalin ƙarfe 3:30 na asuba a ranar Juma’a.

Bisa ga bayanai, dakarun sun mayar da martani cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addan ja da baya.

Makama ya bayyana cewa babu asarar rai ko rauni daga ɓangaren jami’an tsaro da mazauna yankin.

More from this stream

Recomended