Hedikwatar tsaro ta tabbatar da kashe wasu fitattun kwamandojin ‘yan ta’adda hudu a hare-haren da aka kai ta sama cikin mako guda.
Kwamandojin sun hada da Machika, Haro, Dan Muhammadu da Ali Alhaji Alheri, wanda aka fi sani da Kachalla Ali Kawaje.
Daraktan mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Edward Buba, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.
Mista Buba ya bayyana cewa Machika babban kwararre ne a fannin bama-bamai, kuma ƙani ne ga fitaccen dan ta’adda (Dogo Gide) yayin da Haro da Dan Muhammadu suka kware wajen ayyukan garkuwa da mutane.
Ya ce wani farmakin hadin gwiwa da sojojin sama da na kasa suka kai a ranar 11 ga watan Disamba, sun kashe Kachalla Kawaje, wani fitaccen shugaban ‘yan ta’addan da ke da alhakin sace daliban Jami’ar Tarayya ta Gusau, Zamfara.
Ya kara da cewa an kashe Kachalla ne a karamar hukumar Munya ta Jihar Neja tare da wasu dakarunsa.