(Siyasa): Kwankwaso Ya Sanar Da Sabon Dandalin Da Zai Ƙaddamar Da Takarar Shugaban Ƙasarsa A Abuja

[ad_1]








Duk da hana shi yin amfani da dandalin Eagles square dake babban birnin tarayya Abuja don kaddamar da takararsa ta shugaban kasa a zaben shekarar 2019, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai yi kasa a gwiwa ba.

A ranar Talata, 28 ga watan Agusta ne dai manajan dandalin Eagles, Usman Raji ya aikawa kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso cewa basu yarda su gudanar da gangamin a dandalin ba.

Cikin wasikar da ya aika, manaja Raji yace:“sakamakon ranar Laraba rana ce ta aiki, don haka taro kamar wannan na siyasa zai takura ma ma’aikatan gwamnati dake aiki a sakatariyar gwamnatin tarayya, wanda take gab da dandalin.”

Sai dai jaridar Premium Times ta rawaito mai magana da yawun Kwankwaso, Hajiya Binta Sipikin tana cewa sun samu wani sabon wurin da zasu gudanar da gangamin kaddamar da takarar Kwankwaso.

“Gangamin taron kaddamar da takarar shugaban kasa ta Sanata Rabiu Kwankwaso zai gudana ne a ranar Laraba 28 ga watan Agusta a Otal din Chida dake unguwar Utako a Abuja.”Inji ta.

A kwanakin baya ne tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP, sa’annan ya gargadi jam’iyyar PDP da ta tabbata ta mika takarar shugaban kasa ga yankin Arewa maso yamma matukar tana son samun nasara a zaben 2019.




[ad_2]

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...