Sir Alex Ferguson ya koma Old Trafford


Sir Alex Ferguson ya ce yana fatan Manchester United za ta yi nasara idan ya je wasanta da Wolves

.

Manchester United za ta karrama tsohon kociyanta Sir Alex Ferguson a lokacin da zai halarci wasanta a karon farko bayan da aka yi masa tiyata a kwakwalwarsa a watan Mayu.

Ferguson mai shekara 76 zai halarci wasan da United za ta yi na Premier a gida da Wolves a ranar Asabar din nan.

Kungiyar ta bukaci magoya bayanta da su kasance a kujerunsu minti 15 kafin fara wasan, saboda shirin da ta yi na martaba komowar Sir Alex din.

An ruwaito tsohon kociyan yana cewa, ”Ba shakka abu ne da dauki dogon lokaci amma ina murmurewa, ina yin abin da dana ya gaya min na yi da kuma abin da likitoci suka gaya min.”
Zuwan Ferguson filin Old Trafford na karshe tun a ranar 29 ga watan Afrilu, lokacin da ya mika wa tsohon kociyan Arsenal Arsene Wenger kofi na girmamawa.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...